1. “Ku ji abin da ni Ubangijinake cewa,Tashi ku gabatar da ƙararku agaban duwatsu,Ku bar tuddai su ji muryarku.
2. “Ku duwatsu da madawwaman tussanduniya,Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yimuku.Gama Ubangiji, yana da maganagāba da mutanensa,Zai tuhumi Isra'ila.
3. “Ya ku jama'ata, me na yi muku?Wace irin fitina nake yi muku?Ku amsa mini!