6. “Kada su yi wa'azi,” amma sun yiwa'azi.“Idan ba su yi wa'azi a kanabubuwan nan ba,Raini ba zai ƙare ba.
7. Daidai ne a faɗi haka, ya jama'arYakubu?‘Ruhun Ubangiji ya yi rashin haƙurine?Waɗannan ayyukansa ne?’ ”“Ashe, maganata ba takan amfanawanda yake tafiya daidai ba?”
8. Ubangiji ya amsa ya ce,“Ba da daɗewa ba mutanena suntashi kamar maƙiyi,Kukan tuɓe rigar masu wucewa dasalama, masu komawa da yaƙi.
9. Kukan kori matan mutanenaDaga gidajensu masu kyau,Kukan kawar da darajata har abadadaga wurin 'ya'yansu.
10. Ku tashi, ku tafi,Gama nan ba wurin hutawa ba ne,Saboda ƙazantarku wadda take kawomuguwar hallaka.
11. “Idan mutum ya tashi yana iskanci,yana faɗar ƙarya, ya ce,‘Zan yi muku wa'azi game da ruwaninabi da abin sa maye,’To, shi ne zai zama mai wa'azinmutanen nan!
12. “Hakika zan tattara ku duka, yaYakubu,Zan tattara ringin Isra'ila.Zan haɗa su tare kamar tumaki agarke,Kamar garken tumaki a makiyayaZa su zama taron jama'a maihayaniya.