1. Taku ta ƙare, ku masu shiryamugunta,Masu tsara mugunta a gadajensu!Sa'ad da gari ya waye, sai su aikatata,Domin ikon aikatawa yanahannunsu.
2. Sukan yi ƙyashin gonaki da gidaje,sai su ƙwace.Sukan zalunci mutum, su ƙwacegidansa da gādonsa.
3. Domin haka Ubangiji ya ce,Ga shi, yana shirya wa wannanjama'a masifa,Wadda ba za ku iya kuɓuta dagacikinta ba.Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba,Gama mugun lokaci ne.
4. A wannan rana za su yi karinmagana a kanku,Za su yi kuka da baƙin ciki maizafi,Su ce, “An lalatar da mu sarai!Ya sāke rabon mutanena,Ya kawar da shi daga gare ni!Ya ba da gonakinmu ga waɗandasuka ci mu da yaƙi.”
5. Don haka ba za ku sami wanda zai samuku ma'auniA taron jama'ar Ubangiji ba.
6. “Kada su yi wa'azi,” amma sun yiwa'azi.“Idan ba su yi wa'azi a kanabubuwan nan ba,Raini ba zai ƙare ba.