3. Sai waɗansu malaman Attaura suka ce a ransu, “Wannan mutum, ai, saɓo yake!”
4. Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?
5. Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’?
6. Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya”–sai ya ce wa shanyayyen–“Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”
7. Shi kuwa ya tashi ya tafi gida.