1. Da ya shiga jirgi, ya haye ya je garinsu.
2. Sai aka kawo masa wani shanyayye, kwance a gado. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, ka yi farin ciki, an gafarta maka zunubanka.”
3. Sai waɗansu malaman Attaura suka ce a ransu, “Wannan mutum, ai, saɓo yake!”
4. Yesu kuwa, da yake ya san tunaninsu, ya ce, “Don me kuke mugun tunani a zuciyarku?
5. Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya’?