23. Sa'an nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugun aiki.’ ”
24. “Saboda haka, kowa da yake jin maganar nan tawa, yake kuma aikata ta, za a kwatanta shi da mutum mai hikima, wanda ya gina gidansa a kan fā.
25. Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, iska ta taso ta bugi gidan, amma bai faɗi ba, domin an gina shi a kan fā ne.
26. Kowa ya ji maganar nan tawa, bai aikata ta kuma ba, za a misalta shi da wawan mutum, wanda ya gina gidansa a kan rairayi.
27. Da ruwa ya sauko, koguna suka yi cikowa, sai iska ta taso ta bugi gidan har ya rushe, mummunar ragargajewa kuwa!”