9. “Sa'an nan za su bashe ku, a ƙuntata muku, su kuma kashe ku. Duk al'ummai za su ƙi ku saboda sunana.
10. A sa'an nan da yawa za su yi tuntuɓe, su ci amanar juna, su kuma ƙi juna.
11. Annabawan ƙarya da yawa za su firfito, su ɓad da mutane da yawa.
12. Saboda kuma yaɗuwar mugun aiki, sai ƙaunar yawancin mutane ta yi sanyi.
13. Amma duk wanda ya jure har ƙarshe, zai cetu.
14. Za a kuma yi bisharar nan ta Mulkin Sama ko'ina a duniya domin shaida ga dukkan al'ummai. Sa'an nan kuma sai ƙarshen ya zo.”
15. “Don haka sa'ad da kuka ga mummunan aikin saɓo mai banƙyama, wanda Annabi Daniyel ya faɗa, an tsai da shi a Wuri Mai Tsarki (mai karatu fa yă fahimta),
16. to, sai waɗanda suke ƙasar Yahudiya su gudu su shiga duwatsu.
17. Wanda yake soro, kada ya sauko garin ɗaukar wanda yake a gidansa.