Mat 24:18-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Wanda yake a gona kuma, kada ya koma garin ɗaukar mayafinsa.

19. Kaiton masu juna biyu da masu goyo a wannan lokaci!

20. Ku yi addu'a kada gudunku ya zo da damuna, ko ran Asabar.

21. A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.

22. Ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da ba ɗan adam ɗin da zai tsira. Amma sabili da zaɓaɓɓun nan za a taƙaita kwanakin.

23. A sa'an nan kowa ya ce muku, ‘Kun ga, ga Almasihu nan!’ ko, ‘Ga shi can!’ kada ku yarda.

Mat 24