Mat 23:24-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Makafin jagora, kukan tace ƙwaro ɗan mitsil, amma kukan haɗiye raƙumi!

25. “Kaitonku, malaman Attaura da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan ƙwarya da akushi, amma a ciki cike suke da zalunci da zari.

26. Kai makahon Bafarisiye! Sai ka fara tsarkake cikin ƙwaryar da akushin don bayansu ma ya tsarkaka.

Mat 23