Mat 22:37-46 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Ya ce masa, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan hankalinka.

38. Wannan shi ne babban umarni na farko.

39. Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’

40. A kan umarnin nan biyu duk Attaura da koyarwar annabawa suka rataya.”

41. Tun Farisiyawa suna tare gu ɗaya, sai Yesu ya yi musu tambaya,

42. ya ce, “Yaya kuka ɗauki Almasihu? Shi ɗan wane ne?” Sai suka ce masa, “Ɗan Dawuda ne.”

43. Ya ce musu, “To, yaya kuwa Dawuda, ta ikon Ruhu, ya ce da shi Ubangiji? Har ya ce,

44. ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,Zauna a damana,Sai na ɗora ka a kan maƙiyanka.’

45. Tun da Dawuda ya kira shi Ubangiji ne, to, ƙaƙa zai zama ɗansa?”

46. Ba kuwa wanda ya iya tanka masa. Daga ran nan kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin sāke tambayarsa wani abu.

Mat 22