8. Yawancin jama'a suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a hanya.
9. Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!”
10. Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?”
11. Sai jama'a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”
12. Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai.
13. Ya ce musu, “A rubuce yake cewa, ‘Za a kira gidana ɗakin addu'a,’ amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”
14. Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su.
15. Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi.
16. Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa,‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”
17. Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Betanya, ya sauka a can.
18. Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa.
19. Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin 'ya'ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe.