Mat 20:31-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

31. Jama'a suka kwaɓe su su yi shiru. Amma sai ƙara ɗaga murya suke yi ƙwarai da gaske, suna cewa, “Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, ya Ɗan Dawuda!”

32. Sai Yesu ya tsaya, ya yi kiransu ya ce, “Me kuke so in yi muku?”

33. Suka ce masa, “Ya Ubangiji, mu dai mu sami gani!”

34. Domin tausayi, sai Yesu ya taɓa idanunsu, nan take suka gani, suka bi shi.

Mat 20