7. Sai suka ce masa, “To, don me Musa ya yi umarni a ba da takardar kisan aure, a kuma saki matar?”
8. Ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya yardar muku ku saki matanku, amma ba haka yake ba tun farko.
9. Ina kuma gaya muku, kowa ya saki mata tasa, in ba a kan laifin zina ba, ya kuma auri wata, ya yi zina ke nan. Wanda ma ya auri sakakkiya, ya yi zina.”
10. Sai almajiran suka ce masa, “In ko haka tsakanin mutum da mata tasa yake, ashe ma, rashin yin aure ya fi amfani.”
11. Amma ya ce musu, “Ba duk mutum ne zai iya ɗaukar maganar nan ba, sai dai waɗanda aka yardar wa.
12. Akwai waɗanda aka haifa babanni, akwai waɗanda mutane ne suka mai da su babanni. Akwai kuma waɗanda suka mai da kansu babanni domin ƙaunar Mulkin Sama. Duk mai iya ɗaukar maganar nan, yă ɗauka.”