Mat 13:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Yana cikin yafa iri sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su.

5. Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa.

6. Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.

7. Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙaya ta tashi ta sarƙe su.

8. Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba, waɗansu riɓi ɗari ɗari, waɗansu sittin sittin, waɗansu kuma talatin talatin.

9. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

10. Sai almajiran suka zo, suka ce masa, “Me ya sa kake musu magana da misalai?”

11. Ya amsa musu ya ce, “Ku kam, an yarda muku ku san asiran Mulkin Sama, amma su ba a ba su ba.

12. Domin mai abu akan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

13. Shi ya sa nake musu magana da misalai, don ko sun duba ba sa gani, ko sun saurara ba sa ji, ba sa kuma fahimta.

Mat 13