1. A ran nan Yesu ya fita daga gidan, ya je ya zauna a bakin teku.
2. Taro masu yawan gaske suka haɗu a wurinsa, har ya kai shi ga shiga jirgi, ya zauna. Duk taron kuwa suka tsaya a bakin gaci.
3. Sai ya gaggaya musu abubuwa da yawa da misalai, ya ce, “Wani mai shuka ya je shuka.
4. Yana cikin yafa iri sai waɗansu ƙwayoyi suka faɗa a hanya, sai tsuntsaye suka zo suka tsince su.
5. Waɗansu kuma suka faɗa a wuri mai duwatsu inda ba ƙasa da yawa. Nan da nan sai suka tsiro saboda rashin zurfin ƙasa.
6. Da rana fa ta ɗaga, sai suka yanƙwane, da yake ba su da saiwa sosai, suka bushe.
7. Waɗansu kuma suka faɗa cikin ƙaya, sai ƙaya ta tashi ta sarƙe su.
8. Waɗansu kuma suka faɗa a ƙasa mai kyau, suka yi tsaba, waɗansu riɓi ɗari ɗari, waɗansu sittin sittin, waɗansu kuma talatin talatin.
9. Duk mai kunnen ji, yă ji.”