Mat 11:9-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. To, don me kuka fita? Ku ga wani annabi? I, lalle kuwa, har ya fi annabi nesa.

10. Wannan shi ne wanda labarinsa yake rubuce cewa,‘Ga shi, na aiko manzona ya riga ka gaba,Wanda zai shirya maka hanya gabanninka.’

11. Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yahaya Maibaftisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a Mulkin Sama ya fi shi.

12. Tun daga zamanin Yahaya Maibaftisma har ya zuwa yanzu, Mulkin Sama yana shan kutse, masu kutsawa kuwa sukan riske shi.

13. Domin dukan annabawa da Attaura sun yi annabci har ya zuwa kan Yahaya.

14. In kuma za ku karɓa, shi ne Iliya da dā ma zai zo.

15. Duk mai kunnen ji, yă ji.

16. “To, da me zan kwatanta zamanin nan? Kamar yara ne da suke zaune a kasuwa, suna kiran abokan wasansu, suna cewa,

17. ‘Mun busa muku sarewa, ba ku yi rawa ba,Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba!’

18. “Ga shi, Yahaya ya zo, ya ƙi ciye-ciye da shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da iska.’

19. Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka hikimar Allah, ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.”

20. Sai ya fara tsawata wa garuruwan da ya yi yawancin ayyukansa na al'ajabi a cikinsu, don ba su tuba ba.

21. “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.

22. Amma ina gaya muku, a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku.

Mat 11