Mat 11:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya ci gaba daga nan domin ya koyar, yă kuma yi wa'azi a garuruwansu.

2. To, da Yahaya ya ji a kurkuku labarin ayyukan Almasihu, sai ya aiki almajiransa,

3. su ce masa, “Kai ne mai zuwan nan, ko kuwa mu sa ido ga wani?”

Mat 11