1. Bayan 'yan kwanaki, da ya sāke komowa Kafarnahum, sai aka ji labari yana gida.
2. Aka kuwa taru maƙil har ba sauran wuri, ko a bakin ƙofa. Shi kuwa yana yi musu wa'azin Maganar Allah.
3. Sai suka kawo masa wani shanyayye, mutum huɗu suna ɗauke da shi.
4. Da suka kāsa kusatarsa don yawan mutane, suka buɗe rufin soron ta sama da shi. Da suka huda ƙofa kuwa, suka zura gadon da shanyayye yake kwance a kai.
5. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce wa shanyayyen, “Ɗana, an gafarta maka zunubanka.”
6. To, waɗansu malaman Attaura na nan zaune, suna ta wuswasi a zuciya tasu,
7. suna cewa, “Don me mutumin nan yake faɗar haka? Ai, sāɓo yake! Wa yake da ikon gafarta zunubi banda Allah kaɗai?”