Mar 14:71-72 Littafi Mai Tsarki (HAU)

71. Sai ya fara la'antar kansa, yana ta rantserantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan da kuke faɗa ba.”

72. Nan da nan sai zakara ya yi cara ta biyu. Bitrus kuwa ya tuna da maganar da Yesu ya faɗa masa cewa, “Kafin zakara ya yi cara ta biyu, za ka yi musun sanina sau uku.” Ko da ya tuno haka, sai ya fashe da kuka.

Mar 14