Mar 10:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Yesu ya tashi daga nan, ya tafi ƙasar Yahudiya, da kuma hayin Kogin Urdun. Taro kuma ya sāke haɗuwa wurinsa, ya kuma sāke koya musu kamar yadda ya saba.

2. Sai waɗansu Farisiyawa suka zo wajensa don su gwada shi, suka tambaye shi suka ce, “Halal ne mutum ya saki mata tasa?”

3. Sai ya amsa musu ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”

4. Suka ce, “Musa ya ba da izini a rubuta takardar kisan aure, a kuma saki matar.”

5. Yesu ya ce musu, “Don taurinkanku ne Musa ya rubuta muku wannan umarni.

6. Amma tun farkon halitta ‘Allah ya halicce su, namiji da tamata.’

7. ‘Don haka fa sai mutum yă bar uwa tasa da ubansa, yă manne wa mata tasa.

8. Haka su biyun nan su zama jiki guda.’ Har nan gaba su zama ba jiki biyu ba ne, ɗaya ne.

9. Abin da Allah fa ya gama, kada mutum ya raba.”

10. A cikin gida kuma sai almajiransa suka sāke tambayarsa wannan magana.

11. Sai ya ce musu, “Kowa ya saki mata tasa, ya auri wata, zina yake yi da ta biyun.

12. In kuma matar ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

Mar 10