Mak 5:9-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai mun yi kasai da ranmu kafin mu sami abinci,Domin akwai masu kisa a jeji.

10. Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu,Saboda tsananin yunwa.

11. An yi wa mata faɗe a cikin Sihiyona,Haka kuma aka yi wa budurwai a garuruwan Yahuza.

12. An rataye shugabanni da hannuwansu,Ba a kuma girmama dattawa ba.

13. An tilasta wa samari su yi niƙa,Yara kuma suna tagataga da kayan itace.

14. Tsofaffi sun daina zama a dandalin ƙofar birni,Samari kuma sun daina bushe-bushe.

15. Farin cikinmu ya ƙare,Raye-rayenmu sun zama makoki.

16. Rawani ya fāɗi daga kanmu,Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!

17. Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci,Idanunmu kuma suka duhunta.

Mak 5