Mak 5:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Mun miƙa hannu ga Masar da AssuriyaDon mu sami abinci.

7. Ubanninmu sun yi zunubi, ga shi kuwa, ba su,Mu kuwa muna ɗaukar alhakin muguntarsu.

8. Bayi suke mulkinmu,Ba kuwa wanda zai cece mu daga hannunsu.

9. Sai mun yi kasai da ranmu kafin mu sami abinci,Domin akwai masu kisa a jeji.

10. Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu,Saboda tsananin yunwa.

11. An yi wa mata faɗe a cikin Sihiyona,Haka kuma aka yi wa budurwai a garuruwan Yahuza.

12. An rataye shugabanni da hannuwansu,Ba a kuma girmama dattawa ba.

Mak 5