11. An yi wa mata faɗe a cikin Sihiyona,Haka kuma aka yi wa budurwai a garuruwan Yahuza.
12. An rataye shugabanni da hannuwansu,Ba a kuma girmama dattawa ba.
13. An tilasta wa samari su yi niƙa,Yara kuma suna tagataga da kayan itace.
14. Tsofaffi sun daina zama a dandalin ƙofar birni,Samari kuma sun daina bushe-bushe.
15. Farin cikinmu ya ƙare,Raye-rayenmu sun zama makoki.
16. Rawani ya fāɗi daga kanmu,Tamu tu ƙare, gama mun yi zunubi!
17. Saboda wannan zuciyarmu ta ɓaci,Idanunmu kuma suka duhunta.