1. Ya Ubangiji, ka tuna da abin da ya same mu.Ka duba, ka ga yadda muka zama abin kunya!
2. An ba baƙi gādonmu,Gidajenmu kuwa an ba bare.
3. Mun zama marayu, marasa ubanni,Uwayenmu sun zama kamar matan da mazajensu sun mutu.
4. Dole ne mu biya ruwan da za mu sha,Dole ne kuma mu sayi itace.