Mak 3:9-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ya toshe hanyata da sassaƙaƙƙun duwatsu,Ya karkatar da hanyoyina.

10. Ya zamar mini kamar beyar wanda yake fako,Kamar zaki a ɓoye cikin ruƙuƙi.

11. Ya bauɗar da ni daga hanyata, ya yayyage ni,Ya maishe ni, ba ni a kowa.

12. Ya ja bakansa, ya sa in zama abin baratarsa.

13. Ya harbe zuciyata da kiban kwarinsa.

Mak 3