Mak 3:54-66 Littafi Mai Tsarki (HAU)

54. Ruwa ya sha kaina,Sai na ce, ‘Na halaka.’

55. “Ya Ubangiji, na yi kira ga sunankaDaga cikin rami mai zurfi.

56. Ka kuwa ji muryata.Kada ka rufe kunnenka ga jin kukana na neman taimako.

57. Sa'ad da na yi kira gare ka, ka zo kusa.Sa'an nan ka ce mini kada in ji tsoro.

58. “Ka karɓi da'awata, ya Ubangiji,Ka kuwa fanshi raina.

59. Ka ga laifin da aka yi mini,Sai ka shara'anta da'awata, ya Ubangiji.

60. Ka ga dukan irin sakayyarsu,Da dukan dabarun da suke yi mini.

61. “Ya Ubangiji, ka ji zargiDa dukan dabarun da suke yi mini.

62. Leɓunan maƙiyana da tunaninsuSuna gāba da ni dukan yini.

63. Suna raira mini waƙar zambo sa'ad da suke zaune,Da lokacin da suka tashi.

64. “Ya Ubangiji, za ka sāka musu bisa ga ayyukansu,

65. Za ka ba su tattaurar zuciya,La'anarka kuwa za ta zauna a kansu!

66. Da fushi za ka runtume suHar ka hallaka su a duniya, ya Ubangiji!”

Mak 3