Mak 3:41-53 Littafi Mai Tsarki (HAU)

41. Bari mu roƙi Allah na Sama,Muna miƙa hannuwanmu sama, mu ce,

42. “Mun yi zunubi, mun tayar,Kai kuwa ba ka gafarta ba.

43. “Ka yafa fushi, ka runtume mu,Kana karkashe mu ba tausayi.

44. Ka kuma rufe kanka da gajimareDon kada addu'a ta kai wurinka.

45. Ka maishe mu shara da juji a cikin mutane.

46. “Dukan maƙiyanmu suna yi mana ba'a.

47. Tsoro, da wushefe,Da lalatarwa, da hallakarwa sun auka mana.

48. Hawaye suna gangarawa daga idanuna kamar ruwan koguna,Saboda an hallaka mutanena.

49. “Hawayena suna ta gangarawa, ba tsayawa, ba hutawa,

50. Har lokacin da Ubangiji daga Sama ya duba, ya gani.

51. Ganin azabar 'yan matan birninaYa sa ni baƙin ciki.

52. “Waɗanda suke maƙiyana ba daliliSun farauce ni kamar tsuntsu.

53. Sun jefa ni da rai a cikin rami,Suka rufe ni da duwatsu.

Mak 3