34. Ubangiji bai yarda a danne'Yan kurkuku na duniya ba.
35. Bai kuma yarda a hana wa mutum hakkinsaA gaban Maɗaukaki ba,
36. Ko kuwa a karkatar wa mutum da shari'arsa.
37. Wa ya umarta, abin kuwa ya faru,In ba Ubangiji ne ya umarta ba?
38. Ba daga bakin MaɗaukakiAlheri da mugunta suke fitowa ne ba?
39. Don me ɗan adamZai yi gunaguni a kan hukuncin zunubansa?
40. Bari mu jarraba, mu bincika hanyoyinmu,Sa'an nan mu komo wurin Ubangiji.
41. Bari mu roƙi Allah na Sama,Muna miƙa hannuwanmu sama, mu ce,
42. “Mun yi zunubi, mun tayar,Kai kuwa ba ka gafarta ba.
43. “Ka yafa fushi, ka runtume mu,Kana karkashe mu ba tausayi.
44. Ka kuma rufe kanka da gajimareDon kada addu'a ta kai wurinka.
45. Ka maishe mu shara da juji a cikin mutane.
46. “Dukan maƙiyanmu suna yi mana ba'a.
47. Tsoro, da wushefe,Da lalatarwa, da hallakarwa sun auka mana.