Mak 3:30-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Bari ya yarda a mari kumatunsa,Ya haƙura da cin mutunci.

31. Gama Ubangiji ba zai yashe mu har abada ba.

32. Ko da ya sa ɓacin rai,Zai ji tausayi kuma,Saboda tabbatacciyar ƙaunarsa mai yawa.

33. Gama ba da gangan ba ne yakan wahalar da 'yan adamKo ya sa su baƙin ciki.

34. Ubangiji bai yarda a danne'Yan kurkuku na duniya ba.

35. Bai kuma yarda a hana wa mutum hakkinsaA gaban Maɗaukaki ba,

36. Ko kuwa a karkatar wa mutum da shari'arsa.

37. Wa ya umarta, abin kuwa ya faru,In ba Ubangiji ne ya umarta ba?

38. Ba daga bakin MaɗaukakiAlheri da mugunta suke fitowa ne ba?

Mak 3