Mak 3:25-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke sauraronsa,Da wanda suke nemansa kuma.

26. Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,

27. Yana da kyau mutum ya hori kansa tun yana yaro.

28. Bari ya zauna a kaɗaice, ya yi shiruSa'ad da yake da damuwa.

29. Bari ya kwanta cikin ƙura,Watakila akwai sauran sa zuciya.

30. Bari ya yarda a mari kumatunsa,Ya haƙura da cin mutunci.

31. Gama Ubangiji ba zai yashe mu har abada ba.

32. Ko da ya sa ɓacin rai,Zai ji tausayi kuma,Saboda tabbatacciyar ƙaunarsa mai yawa.

Mak 3