Mak 3:24-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Na ce, “Ubangiji shi ne nawa,Saboda haka zan sa zuciya gare shi.”

25. Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke sauraronsa,Da wanda suke nemansa kuma.

26. Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,

27. Yana da kyau mutum ya hori kansa tun yana yaro.

28. Bari ya zauna a kaɗaice, ya yi shiruSa'ad da yake da damuwa.

Mak 3