Mak 3:15-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ya shayar da ni da ruwan ɗaci,Ya ƙosar da ni da abinci mai ɗaci.

16. Ya sa in tauna tsakuwa da haƙorana,Ya zaunar da ni cikin ƙura.

17. An raba ni da salama,Na manta da abar da ake ce da ita wadata.

18. Sai na ce, “Darajata ta ƙare,Ba ni kuma da sa zuciya wurin Ubangiji.”

19. Ka tuna da azabata, da galabaitata,Da ɗacin raina, da kumallon da nake fama da shi.

20. Kullum raina yana tunanin azabaina,Raina kuwa ya karai.

21. Da na tuna da wannan, sai na sa zuciya ga gaba.

22. Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa,Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.

23. Su sababbi ne kowace safiya,Amincinka kuma mai girma ne.

24. Na ce, “Ubangiji shi ne nawa,Saboda haka zan sa zuciya gare shi.”

Mak 3