10. Ya zamar mini kamar beyar wanda yake fako,Kamar zaki a ɓoye cikin ruƙuƙi.
11. Ya bauɗar da ni daga hanyata, ya yayyage ni,Ya maishe ni, ba ni a kowa.
12. Ya ja bakansa, ya sa in zama abin baratarsa.
13. Ya harbe zuciyata da kiban kwarinsa.
14. Na zama abin dariya ga dukan mutane,Dukan yini suna yi mini waƙar zambo.
15. Ya shayar da ni da ruwan ɗaci,Ya ƙosar da ni da abinci mai ɗaci.