1. Ni ne mutumin da ya sha wuyar horon Ubangiji.
2. Ya kore ni zuwa cikin duhu baƙi ƙirin.
3. Hakika ikonsa ya yi ta gāba da ni dukan yini.
4. Ya sa naman jikina da fatar jikina su lalace,Ya kuma kakkarya ƙasusuwana.
5. Ya kewaye ni da yaƙi,Ya rufe ni da baƙin ciki mai tsanani da wahala.
6. Ya zaunar da ni cikin duhu,Kamar waɗanda suka daɗe da mutuwa.
7. Ya kewaye ni da garu don kada in tsere,Ya ɗaure ni da sarƙa mai nauyi.
8. Ko da yake ina kira, ina kukan neman taimako,Ya yi watsi da addu'ata.