38. Ya kori al'ummai a gabanku waɗanda suka fi ku girma da iko, ya kawo ku a ƙasarsu, ya ba ku ita abar gādo kamar yadda yake a yau.
39. Domin haka, yau sai ku sani, ku kuma riƙe a zuciyarku, cewa Ubangiji shi kaɗai ne Allah a sama da duniya. Banda shi, ba wani kuma.
40. Sai ku kiyaye dokokinsa da umarnansa waɗanda na umarce ku da su yau, don zaman lafiyarku da na 'ya'yanku a bayanku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.”
41. Sai Musa ya keɓe birane uku a hayin gabashin Urdun,
42. domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can, wato wanda ya kashe mutum ba da niyya ba, babu kuma ƙiyayya tsakaninsu a dā. In ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen zai tsirar da kansa.
43. Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra'ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.
44. Waɗannan su ne dokokin da Musa ya ba Isra'ilawa,