M. Sh 4:15-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Domin haka, sai ku kula da kanku sosai, gama ba ku ga siffar kome ba sa'ad da Ubangiji Allahnku ya yi magana da ku a Horeb ta tsakiyar wuta.

16. don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,

17. ko siffar dabbar da take a duniya, ko siffar tsuntsun da yake tashi a sararin sama,

M. Sh 4