1. “Ku saurara, ya ku sammai, gama zan yi magana,Bari duniya ta ji maganar bakina.
2. Bari koyarwata ta zubo kamar ruwan sama,Maganata ta faɗo kamar raɓa,Kamar yayyafi a bisa ɗanyar ciyawa,Kamar ɗiɗɗigar ruwa a bisa ganyaye.
3. Gama zan yi shelar sunan Ubangiji,In yabi girman Allahnmu!
4. “Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne,Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne.Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi,Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
5. Sun aikata mugunta a gabansa,Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu,Su muguwar tsara ce, karkatacciya,