M. Sh 29:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Duk da haka har wa yau Ubangiji bai ba ku zuciyar ganewa, ko idanun gani, ko kunnuwan ji ba.

5. Shekara arba'in na bi da ku cikin jeji. Rigunanku da takalmanku ba su tsufa ba.

6. Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku.

M. Sh 29