M. Sh 25:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Idan wata gardama ta tashi tsakanin mutane, suka je gaban shari'a, alƙalai kuwa suka yanke musu maganar, suka kuɓutar da marar laifi, suka kā da mai laifin,

2. idan mai laifin ya cancanci bulala, sai alƙali ya sa shi ya kwanta ƙasa, a bulale shi a gabansa daidai yawan bulalar da ta dace da irin laifin da ya yi.

3. Za a iya yi masa bulala arba'in, amma kada ta fi haka, don kada a ci gaba da bugunsa fiye da haka, har ya zama rainanne a idonku.

M. Sh 25