M. Sh 24:4-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. to, kada mijinta na fari wanda ya sake ta, ya sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Gama wannan abar ƙyama ce a wurin Ubangiji. Kada ku jawo alhaki a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda.

5. “Idan mutum ya yi sabon aure, kada ya tafi yaƙi tare da sojoji, ko kuma a sa shi kowane irin aiki. Sai ya huta a gida har shekara ɗaya saboda gidansa, don ya faranta wa matar da ya auro zuciya.”

6. “Kada mutum ya karɓi jinginar dutsen niƙa ko ɗan dutsen niƙa, gama yin haka karɓar jinginar rai ne.

7. “Idan aka iske mutum yana satar danginsa Ba'isra'ile don ya maishe shi bawansa, ko ya sayar da shi, sai a kashe ɓarawon. Ta haka za ku kawar da mugunta daga tsakiyarku.

8. “Game da ciwon kuturta, sai ku lura ku bi daidai da yadda firistoci na Lawiyawa suka umarce ku, ku yi. Sai ku kiyaye, ku aikata yadda na umarce su.

9. Ku tuna da abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa Maryamu a lokacin da kuka fito daga Masar.

10. “Idan kun ba maƙwabcinku rance na kowane iri, kada ku shiga gidansa don ku ɗauki jingina.

11. Sai ku tsaya a waje, mutumin da kuka ba shi rancen zai kawo muku jinginar.

12. Amma kada ku yarda abin da aka jinginar ya kwana a wurinku idan mutumin matalauci ne.

13. Sai ku mayar masa da shi a faɗuwar rana domin ya yi barci yafe da rigarsa ya gode muku. Yin haka zai zama muku adalci a wurin Ubangiji Allahnku.

M. Sh 24