10. don kada a zubar da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, domin kada alhakin jini ya kama ku.
11. “Amma idan wani mutum yana ƙin wani ya kuwa tafi ya yi fakonsa, ya tasar masa, ya yi masa rauni har ya mutu, sa'an nan ya gudu zuwa ɗaya daga cikin garuruwan nan,
12. sai dattawan garinsu su aiko, a kamo shi daga can, sa'an nan su bashe shi ga mai bin hakkin jini don a kashe shi.
13. Kada ku ji tausayinsa. Ta haka za ku hana zub da jinin marar laifi cikin Isra'ila, don ku sami zaman lafiya.
14. “A cikin gādon da za ku samu a ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku ku mallaka, kada ku ci iyakar maƙwabcinku, wanda kakan kakanni suka riga suka kafa.”
15. “Shaidar mutum ɗaya ba za ta isa a tabbatar, cewa mutum ya yi laifi ba, sai a ji shaidar mutum biyu ko uku, kafin a tabbatar da laifin mutum.
16. Idan ɗan sharri ya ba da shaidar zur a kan wani,
17. sai su biyu ɗin su zo a gaban Ubangiji, su tsaya a gaban firistoci da alƙalai waɗanda suke aiki a lokacin.
18. Sai alƙalan su yi bincike sosai. Idan ɗan sharrin ya ba da shaidar zur a kan ɗaya mutumin,
19. to, sai ku yi masa kamar yadda ya so a yi wa wancan mutumin. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.
20. Sauranku za su ji, su ji tsoro, ba za a ƙara aikata irin wannan mugunta ba.
21. Kada ku ji tausayi, zai zama rai maimakon rai, ido maimakon ido, haƙori maimakon haƙori, hannu maimakon hannu, ƙafa maimakon ƙafa.”