M. Sh 17:18-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Sa'ad da ya hau gadon sarautar, sai ya sa a rubuta masa dokoki daga cikin littafin dokoki wanda yake wurin Lawiyawan da suke firistoci.

19. Kada ya rabu da littafin, amma ya riƙa karanta shi dukan kwanakinsa domin ya koyi tsoron Ubangiji Allahnsa ta wurin kiyaye dukan dokoki da umarnai,

20. don kada zuciyarsa ta kumbura, har ya ga ya fi 'yan'uwansa, don kuma kada ya karkace daga bin umarni zuwa dama ko hagu, don shi da 'ya'yansa su daɗe, suna mulki a Isra'ila.”

M. Sh 17