M. Sh 12:21-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

21. Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku.

22. Kamar yadda akan ci barewa ko mariri haka za ku ci. Marar tsarki da mai tsarki za su iya cin naman.

23. Sai dai ku lura, kada ku ci jinin, gama jinin shi ne rai, kada ku ci ran tare da naman.

24. Kada ku ci jinin, sai ku zubar a ƙasa kamar ruwa.

25. Kada ku ci shi domin ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.

26. Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa'adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa.

27. Sai ku miƙa nama da jinin hadayunku na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji Allahnku. Za ku zuba jinin sadakokinku a bisa bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku ci naman.

28. Ku lura, ku kasa kunne ga dukan umarnan da nake umartarku da su, don ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku har abada, idan kun aikata abin da yake da kyau, daidai ne kuma a gaban Ubangiji Allahnku.”

M. Sh 12