19. Ku lura, kada ku manta da Lawiyawa muddin kuna zaune a ƙasarku.
20. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya fāɗaɗa ƙasarku kamar yadda ya alkawarta muku, sa'an nan ku ce, ‘Ina so in ci nama,’ saboda kuna jin ƙawar nama, to, kuna iya cin nama yadda kuke so.
21. Idan wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa don ya sa sunansa ya yi muku nisa ƙwarai, to, sai ku yanka daga cikin garken shanunku, ko daga tumaki da awaki, waɗanda Ubangiji ya ba ku, kamar yadda na umarce ku. Za ku iya ci yadda kuke bukata a garuruwanku.
22. Kamar yadda akan ci barewa ko mariri haka za ku ci. Marar tsarki da mai tsarki za su iya cin naman.
23. Sai dai ku lura, kada ku ci jinin, gama jinin shi ne rai, kada ku ci ran tare da naman.
24. Kada ku ci jinin, sai ku zubar a ƙasa kamar ruwa.
25. Kada ku ci shi domin ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji.
26. Amma tsarkakakkun abubuwan da suke wajibanku da hadayunku na wa'adi, su ne za ku ɗauka ku kai wurin da Ubangiji ya zaɓa.
27. Sai ku miƙa nama da jinin hadayunku na ƙonawa a bisa bagaden Ubangiji Allahnku. Za ku zuba jinin sadakokinku a bisa bagaden Ubangiji Allahnku, amma za ku ci naman.
28. Ku lura, ku kasa kunne ga dukan umarnan da nake umartarku da su, don ku sami zaman lafiya, ku da zuriyarku a bayanku har abada, idan kun aikata abin da yake da kyau, daidai ne kuma a gaban Ubangiji Allahnku.”
29. “Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kawar muku da al'umman nan waɗanda za ku shiga ƙasarsu don ku kore su, sa'ad da kuka kore su, kun zauna a ƙasarsu,
30. to, sai ku lura, kada ku jarabtu ku kwaikwaye su bayan da an riga an shafe su daga gabanku! Kada ku tambayi labarin kome na gumakansu, ku ce, ‘Ƙaƙa waɗannan al'ummai suka bauta wa gumakansu? Mu ma za mu yi kamar yadda suka yi.’
31. Kada ku yi wa Ubangiji Allahnku haka, gama sun yi wa gumakansu dukan abar ƙyamar da Ubangiji yake ƙi, har sun ƙona wa gumakansu 'ya'yansu mata da maza.
32. “Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku da shi, kada ku ƙara, kada ku rage daga cikinsa.