36. sai dai Kalibu ɗan Yefunne, shi kaɗai ne zai gan ta. Zan ba shi da 'ya'yansa ƙasar da ƙafarsa ta taka, gama shi ne ya bi Ubangiji sosai.’
37. Ubangiji ma ya yi fushi da ni sabili da ku, ya ce, ‘Har kai ma ba za ka shiga ba.
38. Baranka, Joshuwa ɗan Nun, shi ne zai shiga. Sai ka ƙarfafa masa zuciya gama shi ne zai bi da Isra'ilawa, har su amshi ƙasar, su gaje ta.’
39. “Sa'an nan Ubangiji ya ce wa dukanmu, ‘Amma 'ya'yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su ne za su shiga ƙasar. Ni Ubangiji zan ba su su mallake ta.
40. Amma ku, sai ku koma cikin jeji ta hanyar Bahar Maliya.’ ”
41. “Sa'an nan kuka amsa mini, kuka ce, ‘Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi. Za mu tafi mu yi yaƙi bisa ga faɗar Ubangiji Allahnmu.’ Sai kowannenku ya yi ɗamara ya ɗauki makaman yaƙinsa, kuka yi tsammani abu mai sauƙi ne ku shiga ƙasar tuddai.
42. “Amma Ubangiji ya ce mini in faɗa muku, kada ku tafi kada kuma ku yi yaƙi, gama ba ya tare da ku. Maƙiyanku za su kore ku.
43. Haka kuwa na faɗa muku, amma ba ku kasa kunne ba, kuka ƙi yin biyayya da umarnin Ubangiji. Sai kuka yi izgili, kuka hau cikin ƙasar tuddai.
44. Sai Amoriyawa waɗanda suke zaune a ƙasar tuddai suka fito da yawa kamar ƙudan zuma, suka taru a kanku suka bi ku, suka fatattaka ku a Seyir, har zuwa Horma.
45. Sai kuka koma, kuka yi kuka ga Ubangiji, amma Ubangiji bai ji kukanku ba, bai kuma kula da ku ba.