1. Kyakkyawan suna ya fi man ƙanshi tsada, ranar mutuwa kuma ta fi ranar haihuwa.
2. Gara a tafi gidan da ake makokiDa a tafi gidan da ake biki,Gama wannan shi ne ƙarshen dukan mutane.Ya kamata duk mai rai ya riƙe wannan a zuciyarsa,Mutuwa tana jiran kowa.
3. Baƙin ciki ya fi dariya,Gama baƙin ciki yakan kawo gyara.
4. Mai hikima yakan yi tunanin mutuwa,Amma wawa yakan yi tunanin shagalin duniya.
5. Gara mutum ya ji tsautawar mai hikima,Da ya ji wawaye suna yabonsa.
6. Dariyar wawa kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya ce.Wannan ma aikin banza ne.
7. Hakika zalunci yakan sa mai hikima ya zama wawa,Karɓar rashawa kuma yakan lalata hali.
8. Gara ƙarshen abu da farkonsa.Mai haƙuri kuma ya fi mai girmankai.