M. Had 4:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Biyu sun fi ɗaya, gama za su fi samun amfanin wahalar aikinsu.

10. Gama idan ɗaya daga cikinsu ya fāɗi, ɗayan zai taimake shi ya tashi, amma idan ya faɗi yana shi kaɗai, to, tir, domin ba wanda zai taimake shi.

11. Idan mutum biyu sun kwanta tare, za su ji ɗumin juna, amma ƙaƙa mutum ɗaya zai ji ɗumi?

12. Mutum biyu za su iya kāre kansu su ci nasara, amma mutum ɗaya ba zai iya kāre kansa ya ci nasara a kan wanda ya kawo masa hari ba. Igiya riɓi uku tana da wuyar tsinkawa.

15. Na yi tunani a kan dukan mutanen da suke zaune a duniyan nan, sai na gane a cikinsu akwai saurayin da zai maye matsayin sarkin.

16. Mutanen da sarki yake mallaka suna da yawan gaske. Amma bayan ba shi ba wanda zai gode masa saboda ayyukan da ya yi. Hakika wannan ma aikin banza ne, harbin iska kawai.

M. Had 4