1. Sa'an nan na sāke dubawa a kan rashin adalcin da yake ci gaba a duniyan nan. Waɗanda ake zalunta suna kuka, ba kuwa wanda zai taimake su, domin waɗanda suke zaluntarsu suke da iko.
2. Ina ƙyashin waɗanda suka mutu, gama sun fi waɗanda suke da rai yanzu jin daɗi.
3. Amma wanda ya fi su jin daɗi duka, shi ne wanda bai taɓa rayuwa ba, balle ya ga rashin adalcin da yake ta ci gaba a duniyan nan.
4. Na gane dalilin da ya sa mutane suke aiki ƙwarai don su ci nasara, so suke su fi kowa samu. Wannan ma aikin banza ne harbin iska kawai.
13-14. Mutum yana iya tashi daga matsayin talauci ya zama sarki a ƙasarsa, ko ya fita daga kurkuku ya hau gadon sarauta. Amma lokacin da sarki ya tsufa, idan wautarsa ta hana shi karɓar shawara, bai fi saurayin ɗin da yake talaka mai basira ba.