8. Shi ne kuma yake sa lokacin ƙauna, da lokacin ƙiyayya,Da lokacin yaƙi, da lokacin salama.
9. Wace riba mutum zai ci a kan dukan aikinsa?
10. Na san hukuncin da Allah ya ɗora mana mu yi ta fama da shi.
11. Shi ya sa wa kowane abu lokacinsa. Shi ne kuma ya sa mana buri mu san abin da yake nan gaba, amma fa bai ba mu cikakken sanin ayyukan da yake yi ba, tun daga farko har zuwa ƙarshe.
12. Na gane iyakar abin da mutum zai yi, shi ne ya yi farin ciki, ya yi abin kirki tun yana da rai.
13. Dukanmu mu ci, mu sha, mu yi murna da abin da muka yi aikinsa, gama wannan kyautar Allah ce.
14. Na sani dukan abin da Allah ya yi zai dawwama, ba abin da za a ƙara, ko a rage. Allah ya yi haka kuwa domin mutane su zama masu tsoronsa.
15. Dukan abin da ya faru, ya riga ya faru a dā. Allah ya sa abin da ya faru ya yi ta faruwa. Allah yana hukunta abin da ya riga ya faru.