Luk 3:19-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Amma sarki Hirudus, wanda Yahaya ya tsawata wa a kan maganar Hirudiya, matar ɗan'uwansa, da kuma dukan mugayen ayyukan da ya yi,

20. sai ya ƙara da kulle Yahaya a kurkuku.

21. To, da aka yi wa dukan mutane baftisma, Yesu ma aka yi masa baftisma, yana addu'a ke nan, sai sama ta dāre,

22. Ruhu Mai Tsarki ya sauko masa da wata kama, kamar kurciya. Sai aka ji wata murya daga Sama ta ce, “Kai ne Ɗana ƙaunataccena, ina farin ciki da kai ƙwarai,”

23. Yesu kuwa sa'ad da ya fara koyarwa, yana da shekara wajen talatin. An ɗauke shi a kan, wai shi ɗan Yusufu ne, wanda yake ɗan Heli,

24. Heli ɗan Matat, Matat ɗan Lawi, Lawi ɗan Malki, Malki ɗan Yanna, Yanna ɗan Yusufu,

25. Yusufu ɗan Matatiya, Matatiya ɗan Amos, Amos ɗan Nahum, Nahum ɗan Azaliya, Azaliya ɗan Najaya,

Luk 3